Mahara sun kashe dakaci da magidanta biyar a yankin Birnin Gwari

0

Wasu al’ummar kauyen Sarari da ke kusa da garin Kuriga, a Karamar Hukumar Birnin Gwari, sun hadu da fushin mahara, inda suka kashe dakacin kauyen da wasu magidanta su biyar.

Mummunan harin dai sun kai shi ne da misalin karfe 2 na yammacin yau Alhamis, inda aka ji wa wasu mutane takwas mummunan raunuka bayan kisan da aka yi.

Wani da aka ji wa ciwo a kafar sa mai suna Henry, ya tabbatar da mutuwar dakacin kauyen Sarari.

Ya ce maharan sun dira cikin kauyen inda suka rika bi gida-gida su na harbin jama’a.

“To ni dai ban san daga inda suke ba, amma dai kawai mu na zaune, sai muka fara jin karar harbe-harben bindigogi ta kowace kusurwa. Kuma dukkan su a kan babura su ka zo mana, ga su kuma da yawan gaske.

” Sun kashe dakacin kauyen na mu, da wasu magidanta biyar. Sun harbe ni a kafa a lokacin da na ke kokarin tserewa.” Haka Henry ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho.

Henry yace dukkan wadanda aka kashe din maza ne da suka hada da Sule Sarari, wanda shi ne dagacin garin, sai Lado, Yunusa, Jonah, Tela da kuma wani da ya manta sunan sa.

An tafi da dukkan wadanda harin ya ritsa da su asibitin Kula d aLafiya a Matakin Farko, na garin Oduwa, da ke kusa da inda al’amarin ya faru.

Shi ma jami’in kula da marasa lafiya da aka damka su a hannun sa, mai suna Silas Ayuba, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an kai su a asibitin.

Kakakin Gwamnan Kaduna Samuel Aruwan bai amsa kiran neman karin bayani da aka yi masa ba, haka shi ma Aliyu Mukhtar, kakakin ‘yan sandan Jihar Kaduna.

Jama’a da dama dai na mamakin yadda jihohin Kaduna da Zamfara suka gagari cetowa daga munanan hare-haren da tuni masu bin diddigi ke cewa asarar rayukan da aka yi a jihohin a zamanin gwamnatin Buhari, ya fi wadda aka yi zamanin gwamnatin da ta shude.

Wasu kuma mamaki suke yi yadda maharan suka fi bada karfin aiwatar da kashe-kashen su a jihar Kaduna, inda nan ce gida da kuma mazaunar Buhari, ga shi kuma a na wa gwamnan ganin shine dan lelen Buhari, Sai kuma jihar Zamfara inda nan ce mahaifar Ministan tsaro Mansir Dan’Ali. Sai kuma jihar Yobe da aka sace daliban sakandaren Dapchi, inda can ne jihar da ka haifi Babban Hafsan Hafsoshin asakarawan kasar nan, Tukur Butatai.

Share.

game da Author