Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta rawaito cewa mutane 160 sun kamu da cutar Kwalera sannan 13 daga cikin su sun rasu a jihar Yobe.
A dalilin haka gwamnatin jihar ta aika da ma’aikatan kiwon lafiya zuwa kananan hukumomin da ke fama da cutar.
Garuruwar da fama da cutar sun hada da Sabon Gari, Katuzu, Zango, Lawan Musa da Sarkin Hausawa. Sannan kuma za a ci gaba da wayar wa mutane kai kan muhimmancin tsaftace muhalli da sauran su.
Bayan haka an raba magungunan rigakafi kyauta da wayar wa mutane kananan hukumomin Karasuwa da Yusufari da ke kusa da wadannan kananan hukumomin kai don gudun yaduwar cutar.
A karshe shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya aikawa asibitocin dake karamar hukumar Gashua da maganin rigafi da wanda za aba wadanda suka kamu da cutar.
Discussion about this post