Jami’in kungiyar tarayyar kasashen Turai (EU) Chris Udokang ya bayyana cewa tarayyar ta dasa itatuwa sama da miliyan 4 sannan tana kula da su a jihar Katsina.
Ya sanar da haka ne ranar Talata a garin Daura da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya. Bayan haka ya kara da cewa kashi 70 bisa 100 na itatuwan na nan tsaye sai girma suke yi.
” Mun dasa wadannan itatuwa ne a kananan hukumomin Daura, Zango, Mai’adua, Baure, Mashi, Dutsi da Sandamu domin kawo saukin zaizayan kasa da wasu illolin da ke yi wa yanayin kasa barazana.
A karshe Udokang ya ce tarayyar ta gina rijiyoyin burtsatse a wadannan kananan hukumomi domin amfanin mutane da dabbobi sannan da yi wa wadannan itatuwa banruwa.