Kungiyar Obasanjo ta soki Buhari kan yadda ya ke yawon kamfe ana tsakiyar kashe jama’a

0

Hadaddiyar Kungiyar Ceto Najeriya, wadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa, kuma ya ke jagoranta, ta soki Shugaba Muhammadu Buhari kan abin da ta kira yawon kamfe da ya ke yi, duk kuwa da irin yadda ake ci gaba da kashe-kashe a fadin kasar nan, musamman a jihar Benuwai.

Buhari ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takara a zaben 2019, inda da yawan jama’a ke masa kallon ya yi azarbabi, domin ya yi bayanin ne a daidai lokacin da kashe-kashe ke kara muni a yankuna da dama na kasar nan, wadanda bai kai ga magance su ba. Musamman a Benuwai, Zamfara, Filato, Kogi, Borno, Kogi da wasu jihohi.

A cikin wata takarda da kakakin kungiyar, Akin Osuntokun ya fitar, ya ce ziyarar da Buhari ya kai jihar Bauchi inda ya yi kamfe sa’o’i 24 bayan da mahara suka yi mummunan kisa a jihar Benuwai, wani hali ne karara na rashin sanin ya-kamata da ya nuna.

Ya ce bai kamata saboda tsananin kwadayin son ci gaba da mulki, shugaba Buhari ya manta ko ya wofintar da kashe-kashen da ake yi wa ‘yan kasar sa ya tafi yawon kamfe ba.

Kungiyar ta kuma yi wa jama’a matashiya dangane da wani rahoton tsananin take hakkin dan Adam da gwamnatin Amurka ta bayyana ana yi kuma ya na faruwa a Najeriya, karkashin mulkin Buhari.

Dangane da abin da ya faru ga Sanata Dino Melaye kuwa, kungiyar ta kwatanta mulkin Buhari da abin da ta kira, “mulkin Fir’aunanci irin na tsohon shugaban kasar Haiti, Francois Duvelier.”

Share.

game da Author