Fadar Shugaban Kasa ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika kidaya yawan alheran da suka samu a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, maimakon su rika bata lokacin su sauraren kaudin bakin masu kushe gwamnatin.
Babban Kakakin Yada Labaran Gwamnati ne ya bayyana haka, a cikin wata takarda da ya fitar jiya Labara.
Garba Shehu, ya ce gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin tabbatar da cewa kowane dan Najeriya ya ci moriyar canjin da ya zaba a cikin 2015.
“Kaudin muryar masu adawa da kushe gwamnati saboda wata boyayyar manufa ba zai taba zama hijabin da zai makantar da idanun ‘yan Najeriya daga ganin alherin da gwamnatin Buhari ta shimfida ba.” Inji Garba Shehu.
Shehu ya ci gaba da bayyana akasarin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samar wa jama’a a cikin shekaru uku.
Discussion about this post