Kotu ta daure wani magidanci da laifin aikata lalata da karamin Yaro

0

A yau Talata ne kotun majistare dake garin Ikeja jihar Legas ta yanke wa wani mutum mai suna Seyi Olowokere mai shekaru 42 hukuncin zama a kurkukun kirikiri sanadiyyarkama shi da laifin aikata lalata da wani yaro dan shekara 12.

Wanda ya shigar da karar Ezekiel Ayorinde ya bayyana cewa Olowokere ya aikata haka ne a gidan sa dake unguwar Masha Kilo, Surulere ranar 17 ga watan Maris.

Ayorinde ya kuma kara da cewa sun sami labarin haka ne bisa ga bayyana da yaron ya yi wa mahaifiyar sa.

A dalilin haka alkalin kotun Mrs B.O. Osunsanmi ta bada umurnin a daure Olowokere a kurkukun Kirikiri har sai ta kammala sauraron shawarwari daga hukumar gurfanar da mutane masu aikata laifuka irin haka na jihar.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 10 ga watan Afrilu.

Share.

game da Author