Kotu ta daure matar da ta sace jaririya ‘yar wata takwas

0

A yau ne kotun dake Karmo babban birnin tarayya Abuja ta yanke wa wata mata mai suna Theresa Obonna hukuncin zama a kurkuku bayan kamata da laifin sace jaririya ‘yar wata takwas.

Dan sandan da ya shigar da karan Zannah Dalhatu ya bayyana cewa hakan ya faru ne a gidan Theresa dake Jabi a Abuja ranar 2 ga watan Maris.

Ya ce mahaifiyar jaririyar ta fara zama ne da Theresa a watan Janairu 2017 sanadiyar kin cire cikin da saurayin ta ya sa ta yi.

” Bayan watanni takwas da haihuwa sai Theresa kuwa ta sa hannu da dauke wannan jaririya ta gudu.”

Dalhatu yace wani makwabcin su mai suna Godstime David ne ya kawo karan haka a ofishin su a ranar 2 ga watan Maris.

” Nan da nan muka shiga farautar Theresa inda muka kamo ta tare da wannan jaririya.”

A karshe alkalin kotun Abubakar Sadiq ya yanke wa Theresa hukuncin zama a kurkuku sannan ya daga ci gaba da sauraren karan zuwa ranar 3 ga watan Mayu.

Share.

game da Author