Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya gargadi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Kada ya kuskura ya ce ba zai fito takarar Shugaban Kasa a 2019 ba, cewa da zarar Buhari ya ki amincewa da haka, a shirye yake ya maka shi a kotu domin a tilasta masa yin haka.
Ganduje ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa.
” Yanzu a Kano ana ta yi mini kira da in fito takara a 2019 wato 4 + 4, wato in yi Sannan tazarce, kuma dama can ayyukan ci gaba na bukatar isasshen lokaci saboda haka za mu amsa kira mu fito domin ci gaba da ayyukan da muka fara a Jihar.
“Game da Buhari kuwa, mu dai a Kano mun ce sai Shi. Idan ko ya ce ba zai fito takara ba Kotu za ta raba mu.
” A kasar nan mun ga shugaban kasa da ya kashe miliyoyin kudi domin ya zarce Karo na uku, me ko zai sa wanda doka ma ta bashi daman takara yaki yin haka.
Ganduje ya ce yana tare da Buhari kan a ayi zaben shugabannin jam’iyyar kamar yadda take a doka.
Discussion about this post