Ko a cikin barci na ne zan iya mulkin Najeriya fiye da Buhari -Sowore

0

Dandazon magoya baya sun yi wa mawallafin SaharaReporters, Omoyele Sowore kyakkyawar tarba a filin jirgin Murtala Mohammed da ke Legas, yayin da ya iso Najeriya daga New York, na kasar Amurka inda ya ke da zama, domin ya fara shirye-shiryen yakin neman zaben shugaban kasa da zai fara.

Masu tarbar ta sa, wadanda akasarin su matasa ne, da kuma daliban manyan makarantun gaba da sakandare, sun isa filin jirgin kowanen su sanye da riga mai dauke da hoton Sowore, su na ta kida da kuma nuna kwalaye masu rubuce-rubucen kambama mawallafin na SaharaReporters.

Jami’an tsaro sun sha wahalar shawo kan matasan wadanda suka yi kaka-gida a filin jirgin tun kimanin awa daya kafin saukar jirgin Delta Air Lines, wanda ya dauko fasinjoji daga birnin New York zuwa Lagos, ya sauka daidai karfe 2:30 na yamma, dauke har da Sowore.

Fitowar Sowore ke da wuya sai magoya bayan sa suka fara kiran sa da: “Shugaban Kasa.”

A wata gajeruwar tattaunawa da ya yi da manema labarai a filin jrgin, Sowore ya bugi kirjin cewa ai ” shi ko a cikin barci, ko a magagin barci zai yi mulki, to sai ya fi Buhari tabuka abin kirki.”

Ya ci gaba da cewa, idan aka zabe shi, ya zama shugaban Najeriya, to za a ga aiki da cikawa, kuma za a ga fada da cikawa.

Ya ce ya yi niyyar tsayawa takara ne kuma shi kadai kamar tsinken tsire ya fito, ba tare da dafawar wani ubangida ba. Don haka ne ma ya ce ya na so ya ga an kawo karshen siyasar ubangida da ta ‘yan-ba-ni-na-iya, da kuma tsoffin-kwano, masu kewaye shugaban kasa su haka shi aiki.

Da aka tambaye shi don me kai tsaye ya zarce takarar shugaban kasa, maimakon wasu mukamai na kasa da shugaban kasa, sai Sowore ya ce ai shi babu daren da jemage bai gani ba, don haka ya na da gogewar sanin makamar aikin da kasar nan ke bukata.

Sowore ya musanta surutan da wasu ke yi cewa wai wani ofishin siyasa ne zai dauki nauyin sa. Ya ce duk maganganun shirme ne kawai.

“Duk zance banza su ke yi. Ni fa dan jarida ne mai rubuta rahotannin gaskiya, ba na rubuta labaran kanzon kurege. A ce in zauna sai wani ya dauki nauyi na, ai hakan bai ma taso ba. Duk na fi kowane dan takara cancanta, kuma ni ke shirya hanyoyin da magoya baya na ke daddafa min a gidauniyar tallafin kudade.”

Share.

game da Author