Sanata Dino Melaye ya mika sakon godiyar sa ga mutanen ‘Kogi ta Yamma’ da yake wakilta a majalisar dattawa kan jajircewa da suka yi suka na kin kitowa domin a tantance su a shirin kiranye da ake masa.
Idan ba a manta ba jiya ne hukumar zabe ta gudanar da tantance ‘yan mazabun da Sanata Dino ke wakilta, sai dai kuma ba a samu dacewa ba domin sama da Kashi 90 basu fito domin a tantance su ba.
Daga gadon asibiti, Dino ya mika godiyarsa ga mutanen sa sannan ya kikace cewa ba zai karaya ko ya tsorata da abin da ya sa a gaba saboda wannan shiri na wasu sai sun ga bayan sa.
” Allah na tare da ni kuma ba zan hakura ko in tsorata don abin da akayi min yanzu ba. Na san Allah na tare da mai gaskiya.”
Har yanzu dai sanata Dino na asibiti kwance bayan dirowa da yayi daga motar ‘yan sandan a Abuja.