Kakakin hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasa (NHIS) Ayo Osinlu ya bayyana cewa hukumar ta ba asibitoci 23 da suka dakatar wa’adin kwanaki 14 domin su cika sharadun hukumar domin ci gaba da zama a cikin shirin NHIS din.
Ya ce sun yanke shawarar haka ne ranar Alhamis bayan zaman da suka yi da shugabanin asibitocin a Abuja.
Ya kuma kara da cewa idan har wadannan kwanaki suka cika ba tare da wadannan asibitoci sun cika sharaddan ba hukumar NHIS za ta cire su gaba daya daga ciki tsarin shirin hukumar.
Idan ba a manta ba a makon da ta gabata ne hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasa ta dakatar asibitoci 23 cikin 57 a kasar nan ci gaba da zama cikin shirin inshorar kiwon lafiya ta kasa.
Shugaban hukumar gudanarwa na inshoran Enyanatu Ifenne ce ta sanar da haka inda ta bayyaa cewa sun yi haka ne bayan jarabawar da suka gudanar wa duk asibitocin inda suka gano cewa asibitoci 34 ne kawai ke aiwatar da aiyukkan su yadda ya kamata.
” A jarabawar da muka yi wa asibitocin asibiti daya ne a duk fadin kasar nan ta sami maki 100 bisa 100’’.
A dalilin haka ne hukumar ta dakatar da wadannan asibitocin ci gaba da Zama cikin shirin inshorar lafiya domin sabawa dokar gudanar da aiyukkan da shirin ya gindaya