Sojoji na neman mutane biyar bakatatan da ke da hannu a kashe-kashen jihar Taraba

0

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana sanarwar neman wasu mutane biyar da ke da hannu a kashe-kashen jihar Taraba, wadanda ta ce su na da hannu a kashe-kashen da suka faru a Karamar Hukumar Takum da wasu yankunan jihar.

Wadanda ake cigiya din sun hada da Tanko Adiku Dantayi, Danladi Chindo, Big Olumba da Chairman Poko.

Kakakin Sojojin Texas Chukwu ya ce sojoji na kira da duk wanda ya san inda suke ko kuma mai wani karin hasken da zai iya bayarwa domin a cim masu, to ya gaggauta kiran jami’an tsaro.

Dama tun ranar Asabar sojoji sun ce sun samu nasarar damke wasu mutane biyu da suka ce su ne gogarman kisan jama’a a karamar hukumar Ussa a cikin jihar Taraba. Mutanen biyu sun hada Danjuma da kuma Danasabe Gasama.

Chukwu ya ce an cafke Danjuma wanda ake wa lakabi da ‘American’ da shi da Gasama a ranar Juma’a a yankin Takum.

Sojoji sun kara da cewa binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa mutanen biyu manyan gogarman shirya rikicin kashe-kashen da suka faru a kananan hukumomi biyu na Taraba ne.

Share.

game da Author