Karin Wa’adi ya jefa gwamnonin APC cikin rudani

0

Kawunan gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC ya rabu a yau Talata, sakamakon batun karin wa’adin shugabannin jam’iyya.

Bayan taron su da Shugaban Kasa, a yau Talata, sun fito babu wanda ya yi wa manema labarai bayani.

Taron dai sun shafe kimanin awa daya su na zantawa, kuma alamu na nuna cewa taron ya yi zafi sosai.

Bayan taron dai gwamna Rochas Okorocha wanda shi ne shugaban gwamnonin APC, da Abdul’aziz Yari, na gwamnonin Najeriya, sun ki yin magana.

Sai dai kuma wata kwakkwarar majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an yamutsa gashin-baki sosai a wurin taron.

Majiyar ta ce, “ba ta san abin da ake tattaunawa ba, amma dai banda hayaniya da hayagaga kawai a tsakanin su.”

Share.

game da Author