Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya bayyana cewa jihar za ta bukaci dala biliyan 65.5 don samar da ababen more rayuwa da kayata jihar daga nan zuwa shekaru 30 gaba.
Ya fadi haka ne a taron kaddamar da shirin samar da tsarin gina jihar da inganta ababen more rayuwa na shekaru 2018 zuwa 2050 da aka yi a Kaduna ranar Laraba.
Gwamnana ya lissafo yawan kudaden da gwamnati ke bukata domin cimma wanna buri nata da ta sa a gaba, da zai shafi fannonin Ilimi, ayyukan Gona, masana’antu, Kiwon Lafiya da sauran su.
Daga nan sai ya kara da cewa domin samun dauwamammiyar ci gaban da ya kamata dole sai a n sami wadanda zasu saka jari a jihar na gida da waje.
” Abin farin ciki ne in sanar muku cewa jihar Kaduna ta sa sami sama da kashi 75 na masu saka jari daga kasashen waje a cikin shekaru biyun da suka gabata domin ci gaban jihar.”
Bayan haka El-Rufa’I ya kadamar da masana’antar kera taraktoci ‘Springfield Mahindra’ domin bunkasa aiyukkan noma da samun wadatar abinci a jihar.
A karshe shugaban kamfanin, Tarun Das ya ce kamfanin za ta fara aiki nan da watanni biyu ko uku ma su zuwa sannan suna sa ran za su kera taraktoci 3000 duk shekara kuma za ta dibi ma’aikata 200.
El-Rufa’I ya kuma dora tubulin ginin Otel din saukar baki ‘Hilton Hotels’ da za a gina a titin Muhammadu Buhari dake Kaduna.