Kada ku kuskura ku zabi Buhari, ko APC a 2019 – Obasanjo

0

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gargadi ‘yan Najeriya da kada su kuskura su sake zaben Buhari, ko jam’iyyar sa ta APC a 2019.

Obasanjo ya furta haka ne da ya ke karbar bakuntar shugabannin wata kungiya mai suna ‘Sabuwar Najeriya 2019’ a garin Abeokuta, Jihar Ogun.

Obasanjo ya ce APC da Buhari basu tabuka wani tabuka wani abin a zo a gani ba. Saboda haka zaben su kamar sake yin nitso ne a cikin wahala.

” Ku duba ku gani yadda mutane suka fada tsundim cikin tsangwararan wahala, babu Jin dadi da walwala. Gabaki daya shirin tattalin arzikin kasar nan ya darkushe. Ba a gaba- sai dai baya.

” Dole ne dukkan mu mu dawo mu dauki karatun ta natsu, mu gane cewa wannan mulki ba mulkin da za a sake bata dama ba ce. Rike kasar nan ya gagare ta. Mu hada kai gaba dayan mu, mu tumbuke ta. Mu kawo gwamnatin da ke da ainihin ra’ayin talakawa a zukatan su. Nan ne za a kai ga ci.

” PDP ma ba jam’iyyar da za a amince mata bane domin duk kanwar ja ce. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, akwai na kwarai a cikin su wanda suna da kishin kasar nan da talakawa. Gaskiyar magana itace Idan aka sami rudaddiyar gwamnati, duk abin da suka rikito ko jawo, kan mu zai fado, sai ya shafi kowa.  Dole mu karkato da akalar mu dukkan mu mu dau seti, mu mike sambal kan ra’ayi daya domin ceto Najeriya.

” Abin da na fara koya da sani a aikin soja shini, ba a sake mika wa malalaci da wanda ya gaza jagoranci, yin haka sake danka mulki ne a gidan jiya.

A karshe ya roki sauran kungiyoyi da masu kishin Najeriya da a tattaru a matsaya daya a tunkude wannan gwamnati.

Share.

game da Author