Tsohon Mai baiwa Shugaban Kasa Shawara a Harkokin Tsaro, Sambo Dasuki, da ke a tsare yanzu, shi ne ya shirya tsare-tsare kuma ya dauki nauyin yadda aka aiwatar da juyin mulkin 1983, wanda Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa na mulkin soja.
Mustapha Jakolo, tsohon dogarin Buhari ne ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar SUN.
Jakolo, wanda shi ne sarkin Gwandu da aka tube wa rawani, shi ne ya yi wannan ikirari a cikin wani raddi da yayi wa wani littafi da Janar Muhammadu Bashar mai ritaya ya wallafa.
Ya ce a lokacin Dasuki ya na Manjo, shi ne ya rika fadi-tashin nemo kudaden da aka shirya yadda za a dora Buhari kan mulki a matsayin shugaban mulkin soja idan an yi wa Shugaban Kasa na lokacin, Shehu Shagari juyin mulki.
Jakolo yace idan dai ana batun juyin mulkin 1983 ne, to “zance na gaskiya dalili kenan na ke yin kukan zuci a yanzu, idan ina tunanin halin da Sambo Dasuki ke ciki a yanzu. Abin ya na damu na.
“Haka al’amari ke jirkitawa. Idan da ban shigo da Dasuki a cikin shirya juyin mulkin ba, to da batun ma Buhari ya zama shugaba na mulkin soja bai ma taso ba. Sambo ne ya yi ruwa, ya yi tsaki ya ce lallai sai Buhari, ni kuma na goyi bayan sa.
“Na rantse da girman Allah (SWT) Sambo ne ya tsaya kai da fata ya ce sai Buhari. Ni kuma na hada su da Dasuki, kai ko a lokacin da mu ke tsara juyin mulkin, shi ne ke karbo mana kudade wurin Aliyu Gusau, da Hafsan Hafsoshin Sojoji ya taimaka wa juyin mulkin, saboda ba mu samu ko sisi daga Buhari ba.
“Kai Sambo Dasuki bai tsaya a nan ba, sai da ya yi amfani da kudin sa, ya dauki nauyin wasu malamai zuwa Saudi Arebiya su ka yi addu’o’i a Ka’aba domin juyin mulkin ya yi nasara.”
A cikin wani littafi da Yushau Shuaib ya wallafa, “An Encounter with the Spymaster”, Dasuki ya bayyana cewa shi da wasu kananan hafsoshi biyu, wato Manjo Mustapha Jakolo da Manjo Lawal Gwadabe, sun tunkari Buhari da batun shirya juyin mulkin 1983. A lokacin Buhari ya na jagoran Rundunar Najeriya ta 3 a Jos.
Dasuki ya bayyana a cikin littafin cewa shi a ko da yaushe ya rika girmama na gaba da shi, kuma ya na bin umarnin da aka ba shi. Amma duk da haka a lokacin ya na karamin hafsan soja, bai yarda ya bi sauran jami’ai sun je an kamo Buhari a lokacin da aka yi masa juyin mulki.
“Ni dai na hadu da shi ne bayan abin a Bonny Camp lokacin ya na tare da Lawal Rafindadi. Don haka babu yadda za a yi a ce wai ni na kamo Buhari kuma na wulakanta shi. Ina farin ciki saboda har yau akwai wadanda za su iya shaida ta su na nan ba su mutu ba.”
Shi ma tsohon kanar mai ritaya, Abdulmini Aminu, ya tabbatar da cewa ba tare da Sambo Dasuki aka je aka kamo Buhari ba a lokacin da aka yi masa juyin mulki. Haka ya bayyana a cikin wata hira a ya yi da jaridar Sunday Trust, cikin 2015.
Aminu y ace shi ne ya jagoranci kananan hafsoshin da suka kamo Buhari, wato shi da Lawan Gwadabe da John Madaki.
Aminu ya ce shi ne ma ya hau har saman bene ya sauko tare da Buhari suka fita da shi, a cikin girmamawa, ba tare da cin fuska ko wulakanta shi ba.
Discussion about this post