Jami’an tsaro sun kama ‘yan Shara 23 a Kaduna

0

Sanadiyyar rashin zaman lafiya da ayyukan ta’addanci da kungiyoyin matasa da ake kira ‘yan shara a Kaduna da suka hana mazauna unguwannin Kawo, Badarawa, Unguwan Dosa sakat, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Aliyu Mukhtar ya sanar an kama wasu daga cikin wadannan masu tada zaune a Jihar.

Rahotannin da suka iske mu daga bakunan mazauna wadannan unguwanni, mutane sun ga tashin hankali a dan kwanakin nan.

” Matasa da duk basu wuce shekaru 19 ba sun mai da wadannan unguwanni filin yaki.

” Sukan shigo su sheke ayar su babu wanda ya isa ya ce musu kule. Su sari wanda suka gamu dashi sannan wannan karon har kona gidajen abokanan gaba su kayi. Lallai munga tashin hankali matuka.” Inji wani mazaunin Kawo.

Mukhtar ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ba za ta zuba Ido ta bari irin wannan ta’addanci na faruwa a Jihar ba.

Mazauna Jihar Kaduna sun roki gwamnatin Jihar da ta sa Ido sosai game da ayyukan wadannan matasa.

” Abun fa sai addu’a, domin wallahi irin abinda yarannan da ake cewa ‘yan Shara suke yi a ‘yan kwanakinnan ba ya misaltuwa. Da wanda yaji, da wanda bai ji ba duk shafar sa ta keyi. Dole sai gwamnati ta tashi tsaye Kan wannan ta’addanci ci na wadannan matasa.” Inji Hassan Bashir, mazaunin Unguwar Dosa.

Share.

game da Author