Shugaban asibitocin dake shirin inshoran lafiya (HOM) Patrick ya yi kira ga gwamnati da ta samar da kudirorin da za su taimaka wajen samar da ingantaciyyar kiwon lafiya ga kowa a kasar nan.
Ya ce kafa kudirin zai taimaka wajen samar wa mutane da ingantaciyyar kiwon lafiya a duk lokacin da suke bukata batare da sun daga hankulan su game da kudi ba.
A karshe Korie ya koka kan yadda kalilan ne daga ciki mutane ne a Najeriya ke cikin shirin inshoran kiwon lafiya a kasar nan, wanda hakan kamar tauye wa mutanen kasa wani hakki ne da rataya kan gwamnati.
Discussion about this post