INEC ta rantsar da sabbin Kwamishinonin Zabe 7

0

A yau Talata ne Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Zabe na Tarayya guda 7. Wadannan cikon 7 ne ya kai a yanzu ana da kwamishinonin zabe na tarayya 33.

Sabbin kwamishinonin sun hada da Uthman Ajidagba, Kwara; Yahaya Bello, Nasarawa; Emmanuel Hart, Rivers; Mohammed Ibrahim, Gombe da Cyril Omorogbe, Edo. Akwai kuma Baba Yusuf da Segun Agbaje daga jihohin Barno da Ekiti wadanda za su sake ci gaba da kasancewa kwamishinoni a karo na biyu a jere.

Da ya ke rantsar da su, shugaban hukumar Mahmood Yakubu, ya bayyana yakinin sa cewa wadanda ya rantsar din za su taimaka wa hukumar zaben domin a gudanar da zaben da ya fi kowane zabe da aka yi a kasar nan inganci da sahihanci a 2019.

“A yadda n a a ku na da gogewar iya aiki a jami’o’i da ayyukan gwamnati da na masu zaman kan su da ku ka yi, mu na murna da yakininn cewa za ku taka muhimmiyar rawa ga al’umma a fannoni daban-daban.

“Na kuma ji dadin cewa wasun ku sun taba yin aikin zaben a matakin tarayya.”

Daga nan sai Yakubu ya shawarce su da su rika barin kofar su a bude wajen tuntuba da neman hanyoyin samun nasarar ayyukan da aka damka musu amana.

Ya kuma ce baya ga zaben jihar Ekiti da za a gudanar cikin wannan shekarar, akwai wasu zabukan na cike-gurbi har guda 4 da za a gudanar duk a cikin 2018.

Zabukan sun hada da na Mazabar Takun na zaben dan majalisar jiha, sai jihar Kogi inda za a yi zaben cike gurbin dan majalisar Tarayya na Lokoja da Koton Karfe, sai na sanatan shiyyar kudu na jihar Bauchi, sai kuma na shiyyar jihar Katsina, inda a can ne mazabar shugaba muhammadu Buhari.

Daga nan sai Yakubu ya bayyana cewa duk wani wanda ya yi rajistar jefa kuri’a a cikin 2017, to zai iya karbar rajistar sa a satin farko na watan Mayu mai zuwa.

“Amma wadanda suka je su ka yi rajista tsakanin watan Janairu zuwa Maris da kuma wadanda ke ci gaba da yin rajista a yanzu, to za su karbi na su katin zaben na dindindin nan gaba daga baya kafin zaben 2019.’’

Share.

game da Author