INEC ta karyata zargin shirin kirkiro sabbin rumfunan zabe 30,000

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta karyata zargin cewa ta na shirye-shiryen sake kafa sabbin mazabu dubu 30, da nufin taimakawa a yi magudin zabe a 2019.

Jam’iyyar PDP ce ta yi wannan zargin ta bakin kakakin yada labaran ta, Kola Ologbodiyan a ranar Juma’a da ta gabata.

A cikin jawabin da Sakataren Yada Labarai na INEC, Rotimi Oyekanmi ya sa wa hannu jiya Lahadi, ya yi kira da jama’a su yi watsi da abin da ya kira shirmen jawabin da PDP ta yi.

“Abin da kawai muka sani shi ne, INEC ta samu wasiku har guda 3,789 na koke-koken bukatar kara rumfunan zabe a fadin kasar nan.

“Daga nan sai hukumar ta nemi Kwamishinonin Zabe na Jihohi da na Tarayya da su binciki wuraren da ba su da wadatattun rumfunan zabe da kuma inda ba su da rumfar kwata-kwata kuma su na matukar bukata.

Ya kara da cewa an kuma umarce su da su gano yankunan da ke tattare da matsaloli da kalubalen da hakan ce ta sa ba su samu rumfunan zabe a yankin su ba, kuma a gano wadanda rumfunan zaben sun yi matukar nisa daga inda suke.

“Abin da a yanzu muka sani shi ne, har yanzu ana can ana tantance wannan bincike a kowace jiha, rahoton ma bai zo hedikwatar INEC ba tukunna.

Ya ce sai bayan an kammala tattara rahotannin daga kowace jiha, an kawo sannan INEC za ta san irin abin da ya dace a yi.

“Don haka maganganun da ake yi cewa INEC ta kammala shirin kara kirkiro rumfunan zabe 30,000 domin a yi magudin zaben 2019, karya ce, karkatar da hankulan jama’a ne kawai kuma babu wani dalilin yin wannan hujjar zargi ga INEC.”

A karshe ya ce INEC ba za ta taba aiwatar da wani abu wanda ba dokar kasa ce ta bada dama ko umarnin yi ba.

Share.

game da Author