IHU-BAYAN-HARI: ‘Yan sanda 26 sun kewaye gidan Dino Melaye

0

Akalla ‘yan sandan mobayil da kuma sauran karabiti 26 ne har zuwa yanzu ke kewaye da gidan Dino a nan Abuja.

Zagaye gidan na sa ya faru bayan da jami’an shigi-da-fice suka damke shi a filin jirgin Abuja suka hana shi fita kasar zuwa kasar Morocco.

Jami’an sun ce sun kama shi ne saboda ya na cikin jerin sunayen wadanda ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo, kuma aikin su ne duk wanda ake nema ba za su bari ya fita daga kasar nan ba.

Sai dai kuma an saki Dino bayan an kwashe awa biyu da rabi ana casawa. Sannan kuma jami’an ‘yan sanda suka bada sanarwar cewa ba su ne suka kama shi ba.

Da misalin karfe 1:40 kuma sai jami’an ‘yan sanda suka mamaye gidan sa, suka yi wa gidan kawanya.

Wakilin PREMIUM TIMES da ya garzaya gidan, ya kirga jami’an tsaro har 26, da kuma motocin su a gefen gidan daga waje.

Sai dai ba a sani ba ko akwai wasu ‘yan sandan a cikin gidan ko kuma shi ma Dino din ya na ciki ko a’a.

Share.

game da Author