Hukumar kare hakkin ‘yan Najeriya ta saurari karraki 46 a Kano

0

Hukumar kare hakin ‘yan Najeriya na kasa reshen jihar Kano (NHRC) ta bayyana cewa a cikin wata daya hukumar ta saurari kararraki da ya shafi tauye hakin jama’a har 46 a jihar.

Jami’ar hukumar Hauwa Salihu ta fadi haka da take zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Kano.

Hauwa ta ce cikin kararrakin tauye hakin jama’a 46 da suka saurara hukumar ta sasanta 26.

Ta kuma ce hukumar ta fi bada karfi wajen sasanta matsalolin da ya shafi auratayya, rashin kula da yara kanana nuna wariya tsakanin mace da namiji,fyade, rabon gado da dai Sauran su.

A karshe ta ce hukumar kan shigar da kara kotu bayan sun kammala bincike a kai.

Share.

game da Author