Sakamakon batakashin da Boko Haram suka kai wa mazauna Maiduguri da basu samu damar shiga garin ba, an tabbatar da rasuwar mutane 15 sannan wasu 83 sun Sami rauni a harin.
Kakakin rundunar ‘Lafiya Dole’ Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa ” maharan sun nemi shigowa cikin garin Maiduguri Inda suka yi arangama da dakarun mu, daga nan ne fa wasu daga cikin su da suka yi bante da bamabamai suka kutsa cikin jama’a suka tada su.
” Wasu da yawa sun Sami raunuka a sanadiyyar harin. Sannan mun rasa soja daya, amma kuma dakarun mu sun fatattakesu sannan sun kashe mutane 6.
Discussion about this post