‘Gwanin rawa’ Sanata Adeleke ya fito takarar gwamnan jihar Osun

0

Sanata Ademola Adeleke dake wakiltan Osun ta Yamma ya bayyana ra’ayin sa na neman tsayawa takarar gwamnan jihar Osun dake tafe.

Ademola ya bayyana haka ne a wata wasika da PREMIUM TIMES ta gani, sanatan ya ce shine kadai zai Iya daura kambun Dan takarar gwamnan Jihar Osun a PDP ya Kawo kuma kujerar.

” Da na yi takarar Sanata kowa ya gani, sai da na doke Dan takarar gwamnati mai ci, wato dan takaran APC.

Sanata Ademola dai kamar mazari yake, da yaji kida sai ya fara zabura yana murguda jiki, yana rika jejjefa kafafu, babu inda baya motsawa a jikin sa idan yana rawa, kai ko gasar rawa akayi akwai tabbacin Idan bai zo na daya ba, ba ko zai zamo na karshe ba.

Yan takara dai suna ya nuna ra’ayin su na tsayawa takara a zaben gwamnan Jihar da za ayi nan ba da dadewa ba.

Share.

game da Author