Gwamnonin jam’iyyar APC sun sasanta bambance-bambancen da ke tsakanin su, inda a yanzu su ka goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari kan soke karin wa’adin shekara daya da aka yi wa shugabannin jam’iyya.
An cimma wannan matsayi ne a taron su na biyu, da suka gudanar yau Laraba tare da shugaba Buhari. Dama dai jiya Talata sun shafe tsawon lokaci su na tattauna batun, amma aka rabu baram-baram.
Wannan katankatana dai ta kunno kai ne tun bayan da Buhari ya bayyana cewa karin da aka yi musu na wa’adin shekara daya, haramtacce ne ga dokar jam’iyya da kundin dokokin Najeriya.
Da ya ke tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron na yau Laraba, Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari, ya bayyana cewa, “bayan kammala taron da mu ka yi jiya Talata, mun bar ku a cikin duhu, to amma a yau mun tashi mun ga kanun labarai kala daban-daban a jaridu cewa wai an samu rabuwar kawuna a tsakanin mu.
“Wannan ba gaskiya ba ne, mun dai yi taro jiya wanda bayan taron muka shiga mu ka tuntubi shugaban kasa, kuma an daga taron zuwa yau.
“To mun kuma tuntubi dukkan gwamnoni 24 na APC, kuma duk mun amince da shawarar da Shugaba Buhari ya bayar, domin haka kowanen mu zai bi abin da tsarin dokoki ya shimfida.
“Ina sanar muku dukkanmu mun amince a soke karin wa’adin da aka yi wa shugabannin jam’iyya tun daga kananan hukumomi, jiha da tarayya.”
Shi ma shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, a ranar Talata ne ya nada kwamitin mutane 10 a karkashin shugabancin gwamnan Filato, Simon Lalong, da ya dora wa aikin bayar da shawara ga Buhari a kan matakin da ya dauka.
Ya ce za su gabatar da rahoton su a ranar Laraba, wato yau kenan.