Gwamnatin Najeriya ta kara lissafa sunayen wadanda suka wawure kadade

0

Gwamnatin Najeriya ta kara lissafa karin wasu sunayen wadanda ake zargi da wawure kudade a zamanin gwamnatin tsohon mataimakin shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Sunayen na da mutane 23 ne, wadanda Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya bayayyan cewa ya kara fitar da sunayen ne bayan da jama’a suka ce sunayen farko da ya fitar sun yi kadan.

Lai ya ce jama’a sun yi korafin cewa sunayen sun yi kadan, saboda ba su san cewa sunayen farko da aka fitar, somin-tabi kawai aka fara yi, domin a fara da su.

Lai ya kuma kalubalanci PDP da ta ce za ta maka APC kotu. Har ya ke cewa to me kuma PDP za ta yi tsammani idan sun nje kotu?

1. Sambo Dasuki: Dala $2.1 bilyan, sai naira N126 bilyan, wasu sama da Dala $1.5 bilyan sai Fam 5.5 milyan. An rika fitar da akasarin kudaden ne an tumbuza wa kamfanoni, ba tare da an bada wata kwangila ba.

2. Tsohuwar Ministar Fetur, Diezani Alison-Madueke:
Naira bilyan23, sai Dala bilyan $3.

Akwai kuma wasu bilyoyin kudade da akae tuhumar ta tare da Omokore fa Aluko. An kwace dimbin gidaje da kadarorin ta da dama.

3. Janar Kenneth Minimah Mai Ritaya: N13.9 bilyan da kuma wasu Naira bilyan 4.8.

4. Laftanar Janar Azubuike Ihejirika: Naira bilyan 4.5, sai kuma naira N29 milyan.

5. Alex Barde, Tsohon Hafsan Hafsoshin Tsaro: Naira bilyan 8 billion, wadanda tuni har EFCC ta karbo kadarori da kudaden da idan an hada sun kai naira biyan 4.

6. Inde Dikko: Naira bilyan 40, sai kuma wasu naira bilyan 1.1.

7. Air Marshal Adesola Amosun: Naira bilyan 21.4 billion. An kwato naira nilyan N2.8 da gidaje 28 da motoci 3.

8. Sanata Bala Kauran Bauchi, tsohon Ministan Abuja: Naira bilyan 5. Kotu kuma ta bada umarnin rike wasu gidaje na sa kafin a ga yadda shari’a za ta kaya.

9. Sanata Stella Oduah: Naira bilyan 9.8. Ita ma ana rike da wasu kadarori na ta.

10. Babangida Aliyu: Naira bilyan 1.6.

11. Sanata Jonah Jang: Naira biyan 12.5.

12. Bashir Yuguda, tsohon ministan kudade: Naira bilyan 1.5.

13. Sanata Peter Nwaboshi: Naira 1.5 billion

14. Aliyu Usman: yaron Sambo Dasuki: N512 million

15. Ahmad Idris: tsohon PA na Sambo Dasuki: Naira bilyan 1.5.

16. Rasheed Ladoja: Tsohon gwamnan Oyo: Naira milyan 500.

17. Tom Ikimi: Naira milyan 300.

18. Femi Fani-Kayode: Naira milyan 866.

19. Hassan Tukur, tsohon babban sakataren Goodluck Jonathan: Dala milyan $1.7.

20. Nenadi Usman: Naira bilyan1.5.

21. Benedicta Iroha: Naira bilyan N1.7.

22. Aliyu Usman Jawaz: Wani makusancin Sambo Dasuki: Naira mliyan 882.

23. Godknows Igali: Sama da naira bilyan 7.

Share.

game da Author