Gwamnati Kaduna ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 77

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa a cikin shekaru uku da suka wuce ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 77 a jihar.

“A karamar hukumar Kudan an gyara asibitoci biyar, an gyara asibitoci biyu a karamar hukumar Ikara, sannan an gyara asibitoci biyar a karamar hukumar Kubau.

” Sauran kananan hukumomin da aka gyara asibitocin su sun hada da gyara 6 a Zaria, biyu a Lere sannan uku a Sabon gari, da Birnin Gwari.

Rahotan ya kara nuna cewa gwamnati ta gyara asibitoci 20 a kaduna ta Kudu. Wadanda suka rage ba a a gyara ba sune na hukumomin Kaura da Zangon Kataf.

Bayan haka kwamishinan kiwon lafiyar jihar Paul Dogo da yake yin tsokaci kan haka gwamnati ba za tayi kasa-kasa ba wajen ganin ta samar wa mutanen jihar Kaduna da ingantacciyar kiwon lafiya.

A karshe Dogo ya ce gwamanti za ta gyara asibitin Barau Dikko dake Kaduna da makarantar koyan jinya dake Tudun –Wada a Kaduna.

Share.

game da Author