Ba kamar yadda ake ta yadawa ba cewa wai gwamnan Kogi, Yahaya Bello na can a asibiti rai a hannun Allah sanadiyyar sillubowa da yayi daga motar sa, daretan yada labaran gwamnatin jihar Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa wannan batu ba haka take ba.
Kinsley ya ce gwamnan ya sillubo ne a daidai yana kokarin sauka daga motar sa kuma ya samu targade.
” Hakan ya faru ne a lokacin da yake kokarin tarbar kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara a Lokaja.
Ya ce gwamna Yahaya na nan cikin koshin lafiya domin tuni likitocin sa sun daure kafar.