Dole sai shugabanin kasashen Afrika sun zage damtse don kawar da cutar shawara – WHO

0

Shugaban kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Tedros Ghebreyesus ya yi kira ga shugabanin siyasa na kasashen Afrika da su zage damtse don ganin sun kawar da cutar shawara a kasashen su daga nan zuwa 2026.

Ya yi wannan kira ne a taron samun madafa game da cutar wanda kungiyar WHO ta shirya a Abuja ranar Talata inda ya kara da cewa kungiyar a shirye take don hada hannu da kasashen Afrika 37 a kawar da cutar a yankin.

Ghebreyesus ya nuna takaicin sa kan yadda zazzabin shawara ke hallaka mutane a yankin Afrika din ganin cewa za a iya kau dashi ta hanyar yin rigakafi.

” Duk da irin taimakon da kasashen Afrika ke samu daga kungiyoyi da kasashe don kau da cutar har yanzu abin kamar ba ayi ba. Cutar sai kashe mutane ya ke yi.”

Ya ce domin kawar da cutar kungiyoyin WHO, GAVI, Vaccine Alliance, UNICEF da sauran kungiyoyi 50 da suka hada kawance da su za su hada karfi da karfe don ganin sun yi wa mutane biliyan daya allurar rigakafi a kasashen Afrika daga nan zuwa 2026.

Ya ce za su iya samun nasara akan haka ne idan shugabanin siyasa na kasashen Afrika sun mara musu baya kan wannan kokari da suka sa a gaba.

Share.

game da Author