Dino ya diro daga motar ‘yan sanda, an garzaya da shi asibiti

0

A yau da safe ne Dino Melaye ya mika kan sa ga jami’an ‘yan sanda, bayan da suka kwana su na tsare da kofar gidan sa, shi kuma ya kulle kan sa a cikin gidan ya ki fitowa.

Tun jiya ne dai jami’an tsaro kimanin 30 suka yi wa gidan sanatan kwanton-bauna, su na jiran ya fito shi kuma ya yi bagalo a cikin gidan sa.

Safiyar yau Talata ya mika kan sa ga ‘yan sandan da misalin karfe 8 na safe, inda nan da nan suka zarce da shi ofishin zaratan ‘yan sanda masu kai daukin gaggawa ga wuraren da ake aikata muggan laifuka da suka danganci fashi da makami, wato SARS, da ke Guzape, bayan ginin kamfanin da ake buga kudi, NMPC, Garki, Abuja.

Dino Melayi ya sayi tsautsayi da kudin sa, yayin da jami’an tsaro suka dauke shi zuwa Lokoja domin a kai shi can ya amsa tambayoyin zargin a ake yi masa.

Tun kafin a yi nisa, ba a kai ga fita cikin Abuja ba, Dino ya diro daga cikin motar ‘yan sandan da ke dauke da shi, ya fado kasa.

Ganau wanda ya ga sanatan zaune a kasa wasu jamai’an tsaro da matasa sun kewaye shi, a unguwar Area 1, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa wasu matasa ne suka ciccibi Sanatan suka saka shi a wata mota kirar Hilux, suka garzaya da shi asibitin Zankli, da ke Mabushi, Abuja.

Daidai lokacin da PREMIUM TIMES HAUSA ke rubuta wannan labari, Dino ya na kwance asibitin na Zankli. Amma ba a tantance muni ko tsananin ciwon da ya ji ba.

PREMIUM TIMES HAUSA na da kwafen bidiyon da ke nuna Dino Melaye zaune a kasa dirshan kafin wasu da suka zo wurin da yake zaune cikin mota suka ciccibe shi a kai shi asibiti. Kamar yadda wani da yake wurin ya shaida mana.

Shi ma Kwamishinan ‘Yan sanda Jihar Kogi, Ali Janga, ya tabbatar da cewa Dino ya diro daga mota da nufin ya gudu a kan hanyar su ta kai shi Lokoja.

Ya ce amma da ya ke a cikin Abuja ne ya diro, ya na wani asibiti mai suna Zankli, a Abuja.

Ana tuhumar Dino ne da laifin yi wa Shugaban Ma’aikatan Jihar Kogi kazafin cewa ya tura wasu makasa domin su kashe Dino, alhalin kuwa daga baya aka gano cewa karya Dino ya kantara masa a gaban ‘yan sanda.

Baya ga wannan kuma, ana binciken sa da zargin taimaka wa wasu makasa da makamai da kudade domin su tada hankula a jihar.

Wadanda aka kama din ne suka shaida wa ‘yan sanda cewa Dino ne ke daukar nauyin su.

A gefe daya kuma sanatan na fuskantar kiranye daga bangaren INEC tun bayan da wasu jama’ar mazabar sa suka shaida wa INEC cewa sun gaji da wakilcin sa, don haka suna son su musanya shi da wani.

A halin yanzu batun yi masa kiranye ya na a gaban Kotun Koli.

Share.

game da Author