Dino Melaye ya garzaya Kotun Koli

0

Sanata Dino Melaye ya garzaya Kotun Kolin Najeriya, inda a mataki na karshe ya kara daukaka karar hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke wanda ta bai wa INEC iznin a ci gaba da yi masa kiranye.

Melaye wanda shi ne sanatan Kogi ta Yamma, ya tura lauyan sa Mike Ozekome, inda shi kuma ya nemi Kotun Koli da ta biya masa wadansu bukatun da ya zube a gaban ta da suka hada da:

1 – Ya na so Kotun Koli ta hana INEC ci gaba da yi wa Dino Melaye shirin kiranye.

2 – Ya na so Kotun Koli ta haramta sahihancin takardun korafe-korafen da aka yi a kan Dino Melaye, wato a ce duk na bogi ne.

3 – Ya na so Kotun Koli ta yi watsi da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke cewa INEC ta na da iznin yi wa Dino Melaye kiranye.

4 – Ya na so Kotun Koli ta bayyana cewa shi kansa shirye-shiryen kiranyen da INEC ta fara yi a kan sa, haramtacce ne, ba daidai ba ne, domin an kitsa shi ne a cewar sa sakamakon korafe-korafen bogi cike da takardun da aka gabatar wa INEC.

5 – Melaye ya kuma nemi Kotun Koli da ta bayyana cewa wa’adin kwanaki 90 na kiranye ya wuce, don haka haramun ne sake tayar da batun kiranyen.

5 – Yana kuma so Kotun Koli ta karyata Kotun Daukaka Kara da ta ce ba aikin ta ba ne tantance sunayen wadanda suka sa hannun amincewa a yi wa Dino Melaye kiranye. Kotun Daukaka Kara cewa ta yi aikin INEC ne tantancewa, ba aikin kotun ba ne.

6 – Kotun Daukaka Kara a karkashin mai shari’a Tunde Awotoye, tare da wasu alkalai bai biyu, sun yanke hukuncin a ci gaba da yi wa Melaye kiranye.

Share.

game da Author