Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, kuma jigo a jam’iyyar PDP Ibrahim Nasir Mantu ya bayyana cewa dalilan da ya sa ya fadi wa duniya yadda jam’iyyar PDP take murde zabuka a fadin kasar nan shine ganin cewa lokaci yayi da za adawo daga wannan rakiya, a gyara domin ci gaban kasa.
A hira da Mantu yayi da gidan talabijin na Channels, ya ce a lokacin mulkin PDP, sukan shirya magudi ne sosai inda suke ware kudade na musamman domin baiwa jami’an tsaro cin hanci, na jami’an hukumar zaben da bam sannan har wakilan jam’iyyun adawa ma mukan ware musu nasu domin su amince da sakamakon zabe a inda muka ga abin zai bamu wahala.
” Wannan abu mukan shirya su ne domin ‘yan takarar mu su samu nasara a zabukan da ake yi. Na gaji da ganin irin haka na faruwa. Lokaci yayi da za mu maida hankali wajen ganin an gyara wadannan abubuwa da akeyi a da.
” Talauci yayi wa ‘yan Najeriya Katutu, duk inda muka tafi a fadin duniya ana nuna mu kamar marasa gaskiya. Idan ba fadin haka a kayi ba domin a gyara za mu ci gaba da zama cikin rudani ne kawai da karya.