Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yanke shawarar sake tsayawa takara ne, domin ya amsa kiraye-kirayen ‘yan Najeriya masu cewa lallai ya sake tsayawa takara a 2019, ya na mai cewa, ya yanke shawarar ya fara sanar da Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar APC tukunna.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wannan furucin sake tsayawa takara a 2019 ne a ranar Litinin a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar APC a ranar Litinin, wanda a yanzu haka ana can ana gudanar da taro a babbar sakatariyar APC a Abuja.
Ya yi wannan furucin ne bayan da ‘yan jarida suka fita daga dakin taron.
Shugaban Masu rinjaye a amajalisar tarayya, Hon. Ado Doguwa daga Kano, ya tabbarar wa PREMIUM TIMES bukatar Buhari ta sake tsakaya takara.
Ya yi bayanin aniyar ta sa ce ta sake tsayawa takara kafin ya karanta bayanin sa.
A jawabin na sa, Buhari ya ce ya kamata APC ta tsaya a kan alamar ta ta tsintsiya madaurin ki daya, a ci gaba da hadin kai, domin ganin zabe ya gabato, nasara ba ta samuwa sai da magoya baya masu yawa.
Ya kuma ce dukkan shugabannin da za su sauka kowane ya na da damar sake tsayawa takarar mukamai.
Ya kara jaddada cewa matsayin da ya dauka na kara wa jam’iyyar karfi ne da dankon hadin kai, ban a raba kawuna da kawo bambance-bambace ba. Ya na mai nuni da cewa tunanin sake zaben zai kawo karshen tirka-tirkar da za a iya
fuskanta ganin wasu sun garzaya kotu saboda ba su yarda a yi karin wa’adi ga shugabanni ba.
Ya ce amma tunda za a sake zabe, ai duk wata shari’a ta kare kenan.