Daliban makarantar Chibok 30 suka rage a raye ba 15 ba – Salkida

0

Mako daya bayan dan jarida Ahmed Salkida ya bada sanarwar cewa dalibai 15 ne kadai daga cikin dalibai 113 ‘yan makarantar da ke hannun Boko Haram suka rage a raye, a yau kuma ya bada hakuri cewa alkaluman da ya bayar akwai kuskure, 30 ne suka rage.

A wani sako da ya tura a shafin sa na tiwita, ya ce ‘yan mata 30 ne suka rage daga cikin 113, ba 15 ba kamar yadda ya bayyana da farko.

Salkida ya kara da cewa ya na bai wa jama’a hakurin kuskuren da ya yi na bada adalin daliban da suka rage ba daidai ba.

Idan za a iya tunawa, bayan ya fitar da waccan sanarwa inda ya ce dalibai 15 ne suka rage, gwamnatin tarayya ta maida masa amsa cewa ba za ta tsaya cacar baki da shi ba, amma dai za ta ci gaba da kokarin ceto dukkan wadanda ke hannun Boko Haram.

Shi kuma Salkida ya ce dalilin da ya sa ya fitar da sanarwar adadin wadanda ke da sauran rai, ya yi ne domin Boko Haram da Gwmmantin Najeriya su fito da adadin hakikanin wadanda suka rage domin a tabbatar.

Ya ce sakonnin da ya rika turawa ne a baya suka sa har Boko Haram suka fito suka bayyana yawan adadin wadanda suke rike.

Salkida ya ce da farko majiyar sa a cikin Boko Haram ta sanar da shi cewa yara 15 suke a tsare, amma daga bisani ya ce majiyar ta kara shaida masa cewa ashe bai sani ba akwai wasu daliban mata 10 a tsare a wani wurin a tsare, sai kuma wasu 5 da ke tsare daban.

Share.

game da Author