Buhari ya sa hannun amincewa a sayo makamai na dala biliyan daya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa a sayo makamai na dalar Amurka biliyan daya, kwatankwacin sama da naira biliyan 300.

Ministan Tsaro Mansur Dan’Ali ne ya bayyana wa manema labarai a lokacin da ya ke zantawa da su a fadar shugaban kasa, jim kadan bayan kammala taro kan batutuwan tsaro wanda shugaban kasa da kan sa ya jagoranta.

Dan’Ali ya kara da cewa taron kamar dai irin wanda suka saba yi ne kan tsaro tsakanin shugaban kasa da sauran hukumomin tsaron kasar nan.

Mun tattauna abubuwan da suka shafi jihohi, musamman abin da ake ciki a Zamfara, Taraba da wasu jihohi.” Inji shi.

Ya ce sauye-sauyen da aka samu da kuma tura jami’ai a jihohi kamar Zamfara da sauran wadanda ke makwabtaka da ita, kamar Sokoto da Katsina ana kyautata yakinin yin hakan zai shawo kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankunan.

Ya ce an tsaurara matakan tsaro har da ta sararin sama a yankunan.

Da ya ke magana a kan Leah Sharibu, dalibar Dapchi da ta rage a hannun Boko Haram, Dan’Ali ya ce suna bakin kokarin ganin ta dawo gida lafiya.

Share.

game da Author