Boko Haram sun fara karbar haraji hankalin su kwance yankunan Borno, Yobe

0

Boko Haram ta fara karbar harajin da ta ke kira ‘jizya’ a wasu matsugunai na yankunan Barno, Yobe da kuma yankin Tafkin Chadi, inda tuni ‘yan kungiyar ke gudanar da mulkin yankunan a karkashin irin dokokin su, ba dokar Najeriya ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ne ya ruwaito labarin.

Reuters ya ruwaito a jiya Lahadi cewa, wani yankin Boko Haram da ya balle ya ke cin gashin-kansa, mai suna ISWA, a yanzu shi ke rike da wasu yankuna da akalla sun kai fadin murabba’in kilomita 160 a cikin jihohin Barno da Yobe.

Rahoton ya ci gaba da cewa manoma da makiyayan yankin sun yi kukan cewa ana karbar harajin ‘jizya’ na naira 2,500 ga kowane sa ko saniya daya. Yayin da sauran dabbobi kuma kamar tumaki da awaki ana biya musu naira 1,500 kowace daya.

An kuma ruwaito cewa Boko Haram din sun kafa mayanka inda suke yanka shanu, inda suke kula da ko guda nawa ake yankawa a kullum, kuma su na kula da batun saran dazuka da masu saran itacen girki ke yi.

“Idan kai makiyayi ne, ko direba ko dan tireda, ba za su taba ka ba, amma abin da kawai su ke so shi ne ka bi umarni da dokokin su.’ Haka wani makiyayi ya bayyana wa Reuters, kuma ya roki a sakaya sunan sa.

Ma’aikatan tsaron Najeriya ba su karyata labarin cewa Boko Haram na karbar haraji a hannu jama’a, amma ta musanta batun cewa su na rike da wani sashi na kasar nan.

Share.

game da Author