BINCIKE: Rashin samun isasshen barci na kawo cutar yawan mantuwa

0

Wasu likitoci a makarantar ‘American National Institute on Alcohol Abuse and Alcoholism (NIAAA)’dake kasar Amurka sun bayyana cewa rashin samun isasshen barci na kawo cutar ‘Alzheimer’.

Cutar Alzeheimer, cuta ce dake sa mutum yana manta abu a hankali – a hankali, kafin ya ankara sai kaga ba ya iya tuna wasu abubuwa da ya kamata ace yana iya tunawa.

Shugaban likitocin Nora .D. Volkow ta ce cutar ‘Alzheimer’ na kawo yawan mantuwa da wasu canje-canje wajen yanayin mutum sannan bincike ya nuna cewa cutar ta kama sama da mutane miliyan 5.7 a Amurka.

Sanadiyyar hakan ne suka yi kira ga mutane da su guji hana kan su samun isasshen barci domin guje wa kamuwa da wannan cutar

Share.

game da Author