A wani bincike da wasu likitocin kasar Britaniya su ka gunar, sun gano sabuwar maganin kawar da zazzabin cizon sauro mai suna ‘Ivermectin’ dake iya ba mutum rigakafi har na wata daya sannan idan sauro ya ciji mutum shima zai mutu.
Jagoran wadannan likitoci Menno Smit ya bayyana cewa maganin za ta yi aiki ne a jikin mutum kamar alluran rigakafin cutar saboda ingancin kariya da take da ita da zai yi kwanaki talatin yana aiki a jikin mutum.
Ya ce idan mutum ya hadiyi maganin jinin sa na zama guba wa sauro yadda a duk lokacin da ya ciji mutum shima da kan sa mutuwa zai yi.
Smit ya bayyana cewa bayan sun hada maganin sun gudanar da gwaji akai da wasu marasa lafiya a kasar Kenya wanda bayan sun sha maganin sai suka dibi jinin su suka shayar da wasu sauro da suka killace. Bayan hakan sai sauron suka mutu da suka sha wannan jini.
” Hakan da muka yi ya kashe mafi yawan sauron da muka killace domin yin wannan gwaji.”
A karshe ya ce wannan magani da suka binciko zai taimaka wa musamman mutanen kasahen Afrika da ke fama da wannan cuta.
Discussion about this post