Ba bu inda a ke siyar da kifin roba a kasuwanin Najeriya- NAFDAC

0

Hukumar (NAFDAC) ta yi shelar cewa babu kasuwar da ake siyar da kifin roba a kasar nan kamar yadda ake ta yadawa a wasu sassan kasar nan musamman ta kafafen yada labarai na yanar gizo.

Hukumar ta yi wannan sanarwa ne ranar Alhamis a Abuja bayan rahotanni da ya iske ta cewa wai ana siyar wa mutane da kifin roba a kasuwannin kasar nan.

Hukumar ta ce bayan ta saurari rahotan ne ta gudanar da bincike sannan ta gano cewa kifin ba na roba bane sannan kifin ya ki dahuwa ne saboda kamuwa da wasu kwayoyin cututtuka da ake kira ‘Bacteria’.

Hukumar ta yi kira ga mutane da su kula da irin abincin da suke ci sannan ta tabbatar da cewa babu kasuwa a Najeriya da ke siyar da kifin roba.

Share.

game da Author