AURE NA: kila ‘yar gida za a yi – Sheikh Isah Alolo

0

A hira da PREMIUM TIMES HAUSA tayi da shahararren dan wasan fina-finan Hausa, furodusa kuma mai ba da umarni, wato darekta Sheikh Isa Alolo daga Abuja, Jarumin ya bayyana wa jaridar dalilan da ya sa ya tsunduma cikin harkar shirya fina-finan Hausa.

Bayan haka ya fadi mana irin mace da yake shirin ya aura, kuma kila ma ‘yar gida za a yi in Allah ya yarda.

PT: Kowa dai yasan cewa malami ne ake yi wa lakani da Sheikh, Yaya akayi ka samu naka sheikh din, ko dama can shehi ne?

Sheikh: A’a ni dai musulmi ne na kwarai sannan mai kula da addinin sa. Ina iya kokari na wajen ganin duk abin da na sa a gaba na kan yi kokari in ga nayi fice akai. A haka a haka ne har aka rada mini wannan lakani.

PT: Yaya kake ji idan aka kira ka da wannan suna?

Sheikh: Ji nake kamar wan shugaban kasa, tun da suna ne mai kyau. Ina jin dadin haka.

PT: Yaya akayi ka fara harkar fina-finai?

Sheikh: Tun Ina yaro nake sha’awar shiga harkar fim, kamar yadda duk wani akto ke fadi amma sai dai nawa da dan bambamci domin na fara da yin kwalliya ne daga nan sai na fara yin gaba-gaba har na kawo inda nake yanzu.

PT: Ina kake yanzu?

Sheikh: Ni yanzu akto ne, furodusa, kuma darekta.

PT: Ba ka ganin aiki zai iya maka yawa, ganin wadannan abubuwa da aka ambato duk suna bukatar maida hankali?

Sheikh: Haka ne, sai dai yanzu na fi maida hankali ne wajen harkar darektin.

PT: To yaya maganar harkar kwalliya?

Sheikh: Bana yin kwalliya yanzu, sai dai na kan dan leka sama-sama, amma bashi nake yi ba.

PT: Fim nawa ka yi zuwa yanzu?

Sheikh: Gaskiya bazan iya tunawa ba yanzu, amma na san tabbas ya wuce 100.

PT: Wanne ne yafi baka wahala?

Sheikh: ‘KIJE KYA GANI’, bazan taba mantawa da wannan fim din ba. Na yi matukar wahala a wannan fim. Bayan makudan kudi da na kashe a fim din, a wannan karo ne na fara fita daga kano domin zuwa wuraren da zan yi amfani dasu wajen yin fim din. A haka ma an yi ta kai ruwa rana sannan kuma mun sha tsananin wahala. Bayan haka ba karamin hasara nayi ba.

Fim din bai yi kasuwa ba kwata-kwata. Kai a lokacin saura kadan in hakura da harkar fina-finai.

PT: Wani fim ne ya fi faranta maka rai?

Sheikh: ‘UWAR GULMA’ Wannan fim yayi min dadi, fim ne da komai da nayi a fim din ya karbu. Na shana sosai da wannan fim din. Abin dai Allah ne ya saka min da wahalar da na sha a wancan lokacin da hakuri da nayi.

PT: Kana sha’awar fitowa a fina-finai na barkwanci, me ya sa haka?

Sheikh: Ina da shawa’ar sa mutane nishadi, shine ya sa nake son haka. Ina so in ga mutane cikin farin ciki a ko wani lokaci, shine ya sa nake fitowa a irin wadannan fim din.

PT: ko kayi aure?

Sheikh: A’a, bani da mata sai dai ina kokarin ganin na yi aure nan ba da dadewa ba, kuma ina ganin ‘yar gida nake sa ran za a yi, wato kila ma taurariyar Kannywood ce. Sai dai kun gani.

Daga karshe ina so inyi amfani da wannan dama domin jinjinawa gidan jaridar PREMIUM TIMES da kokari da take yin a yada ayyukan mu a kannywood. Muna godiya.

Share.

game da Author