APC: Fayemi ya fito takarar gwamnan jihar Ekiti

0

Ministan Ma’adinai Kayode Fayemi ya rubuta wa hedikwatar jam’iyyar sa ta APC cewa zai yi takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar.

Za a yi zaben gwmanan jihar Ekiti ne ranar 12 ga watan Yuli mai zuwa.

Idan ba a manta ba Fayemi ya fadi zaben neman ta zarce shekaru hudu da suka wuce in da dan takarar PDP Ayo Fayose ya lashe zaben.

Fayemi ya rubuta wasikar sanar da haka ne ga shugaban jam’iyyar John Oyegun sannan ya sanar da wasu gaggan jam’iyyar da ya hada da Bola Tinubu, Bisi Akande da sauran su.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba da walakin za ayi barambarama a zaben dan takarar jam’iyyar domin shima mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu maso yamma da shima tsohon gwamnan jihar ne, Segun Oni ya siya fom din takarar gwamnan jihar.

Zuwa yanzu dai ‘yan takara 35 ne daga jam’iyyar APC ke neman tsaya takarar gwamnan jihar.

Share.

game da Author