Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Chike Oti ya bayyana cewa ma’aikatan su dake sintiri a kasuwar Oluwole dake Apapa sun kama wani tsoho mai shekaru 80 daidai ya na kokarin sace wasu yara uku.
” Wani da abin ya faru a idon sa mai suna Adetunji Salami yace ya hango yaran sun fara bin tsohon cikin kwalekwalen sa bayan ya shafa goshin yaran da kudi.
” Ina ganin haka kuwa sai na yanka Ihu, mutane kuwa suka taro shi maza-maza.”
” Bayan ya sha dukan tsiya, da kyar ‘yan sanda suka ceto shi daga hannun mutane.
Oti ya kara da cewa daya daga cikin yaran da aka sace ya tabbatar wa ‘yan sanda da aukuwar haka.
Discussion about this post