Masu garkuwa da mutane a Najeriya sun kama wani Bature sun yi garkuwa da shi, wanda ke aiki a kamfanin Dantata and Sawoe a Kano.
An kama Baturen wanda Injiniya ne a Kano, bayan an bindige wani jami’in ‘yan sanda.
Ganau da aka yi abin a kan idon sa ya tabbatar da cewa maharan sun yi amfani da wata motar haya ce kirar Golf, inda daga cikin ta ne su ka bude wa dan sandan wuta suka kashe shi, daga nan suka sace Baturen.
Wani jami’in tsaro da ke kula da kayan aikin kamfanin ya shaida wa manema labarai cewa al’amarin ya faru ne a yau Litinin da safe a lokacin da su ke kusa da fara aiki.
Ya kara da cewa an kuma samu akasi inda wani harsashi ya yi tsalle ya samu daya daga cikin direbobin kamfanin.
“Su dama maharan su na zuwa ba su yi wata-wata ba sai kawai su ka fara bude wuta, suka kashe dan sandan wanda mobayil ne, wanda ke kula da tsaron Baturen.
Kakakin yada labaran rundunar ‘yan sandan Kano, Majia, ya bayyana cewa makasan su biyar ne wanda su ka kai harin sace Baturen mai aiki a kamfanin Dantata and Sawoe da misalin karfe 7:45 na safiyar Litinin.
Ya ce jami’in dan sandan da aka kashe din saje ne.
Kwamishinan ‘Yan sandan Kano, Rabi’u Yusuf, ya shaida cewa an kafa zaratan ‘yan sandan da aka bai wa umarnin nemo duk inda aka tsare shi tare da kamo wadanda suka yi garkuwar da shi.
Rundunar ta kuma yi kira ga duk wanda ke da rahoton wani bayani da zai taimaka wajen yin nasarar gano su, to ya buga wadannan lambobi: 08032419754, 08123821575.