An yi batakashi tsakanin sojoji da mahara a Zamfara

0

An bada rahoton kashe sojoji biyu da mahara da dama, a wani batakashi da suka yi a cikin dajin Karamar Hukumar Anka, cikin Jihar Zamfara.

Gumurzun dai ya faru ne a ranar Labara, kamar yadda Shugaban Karamar Hukumar Anka, Mustapha Gado ya bayayyana wa PREMIUM TIMES.

Gado yace, wanda ya bayyana kashe sojojin biyu, ya ce rahoto ya je masa cewa sojoji sun kashe marahan da dama.

“Mun ga gawarwakin sojojin biyu, mun kuma samu labarin cewa sojojin sun kashe maharan da dama. A cikin sojojin an ce mana daya kaftin ne, daya kuma karamin ofisa ne.

“Na kuma samu labarin cewa karo tulin sojojin da aka yi, an samu nasarar karkashe mahara da daman gaske.”

Tun bayan kashe sama da mutane 50 da aka yi dai gwamna Abdul’azia Yari ya bai wa jami’an tsaro umarnin cewa duk wanda suka kama da makami a daji, to a harbe shi kawai.

Share.

game da Author