Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci da ke Magajin Gari a Kaduna, ta yanke hukuncin Bulala 80 kan Shu’aibu Umar, wanda aka kama da laifin zargin matar yayan sa, inda ya yi furta cewa karuwa ce.
Matar mai suna Suwaiba Abdulkadir, ta shigar da kara ne, inda ta nemi a bi mata hakkin ta ga kanin mijin na ta, wanda ya yi mata kazafi daga sabani ya shiga tsakanin su.
“Ina neman kotu ta yi a dalci, ta bi min hakki na, saboda daga sabani ya shiga tsakanin mu, sai ya kira ni da suna karuwa.” Inji Suwaiba.
Shi kuma wanda ake kara, bai yi gardama ba, ya furta cewa ya kira ta karuwa a cikin fushi, amma kuma ya shaida wa kotun cewa shi fa bai yi nadamar kiran ta karuwa da ya yi ba.
“Ni ma din ai ban ji dadi ba da ta kira ni dan kwaya, kuma ta kira ni barawo, dalili kenan na kira ta karuwa. Kuma ni ba zan nemi afuwa ko na janye kiran ta karuwa da nayi ba.” Inji Sha’aibu Umar.
Alkali Dahiru Lawal ya yanke masa hukuncin a tsala masa bulala 80 saboda kiran ta karuwa da ya yi, bayan alkalin ya nemi ya janye furucin da ya yi, amma ya ce ya na nan kan bakan sa.