An sako shugaban kungiyar direbobi da aka sace a Birnin Gwari

0

Masu garkuwa sun sako ‘yan kungiyar direbobi ‘NURTW’ da suka yi garkuwa da a hanyar Kaduna zuwa Funtuwa.

An sako wadannan mutane ne wanda ya hada da shugaban kungiyar na shiyyar Birnin Gwari Abdu Kano tare da sauran ‘yan kungiyar su biyar ranar Talata da misalin karfe 12 dare.

Idan ba a manta ba ranar Juma’ar da ta gabata ne PREMIUM TIMES ta Kawo muku rahoton cewa wasu masu garkuwa sun sace ‘yan kungiyar direbobin a hanyar su na dawowa Birnin Gwari daga Funtuwa ranar Alhamis.

Sakataren kungiyar Al’Mustapha Ahmad ya tabbatar da haka wa PREMIUM TIMES ta wayan tarho da safiyar Talata inda ya kara da cewa sai da suka biya kudin fansa har Naira miliyan biyar kafin aka sako su.

“Barayin sun sako ‘yan kungiyar mu da suka sace a hanyar Funtuwa bayan mun biya Naira miliyan biyar sannan sun yi mako daya suna tsare.”

Ahmad ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo karshen wannan matsala da matafiya ke fama da shi a hanyar Funtuwa sannan ya yi kira ga matafiya musamman direbobi da su guji bin wannan hanya da zaran karfe 4 na yamma ta yi.

Share.

game da Author