An sako amaren da aka sace a Birnin-Gwari

0

Idan ba a manta ba ranar Asabar din da ta gabata ne gidan PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa masu garkuwa sun waske ta amarya da kawayen ta a hanyar kai ta gidan miji a karamar hukumar Birnin Gwari.

Yanzu dai amaryar da kawayen ta sun koma gidajen su bayan sako su da masu garkuwan suka yi ranar Alhamis da karfe 8:30 na dare sai dai babu tabbacin ko an biya su kudin fansa ko a’a.

Shugabannin al’umma da mutanen gari sun yi kira ga gwamnati da su taimakawa jama’a da samar da tsaro wa mutanen yankin .

Share.

game da Author