An sace Sakataren PDP

0

Masu garkuwa da mutane sun sace Sakataren Kudi na Jam’iyyar PDP a Jihar Ekiti, Kayode Oni.

Rahotanni sun ce an sace Oni a kan babban titin Efon Alaaye zuwa Ekiti, a lokacin da ya ke komawa gida daga garin Aremoko Ekiti, hedikwatar karamar hukumar Ekiti ta Yamma cikin daren ranar Asabar.

Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar PDP na jihar, Jackson Adwebayo, ya tabbatar da faruwar mummnan lamarin.

A jiya Lahadi ya ce Oni ya je karamar hukumar ce domin gudanar da taron jam’iyya inda za a yi zaben shugabannin jam’iyya na karamar hukuma.

Adebayo ya ce wadanda suka yi garkuwar da shi su na neman naira miliyan 30 kafin su sake shi. Ya ce haka suka shaida wa matar sa da kuma kanin sa.

A lokacin da aka sace shi, ya na tare da ‘yar sa daya da wani jikan sa a cikin motar.

Adebayo ya ce iyalan Oni sun kasa hada ko da naira miliyan daya, amma su wadanda suka sace shi, sun ce sai an biya naira miliyan 30.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Abdullahi Tsafe ya ce a ba shi lokaci kafin ya ce wani abu, domin ba ya gari.

Haka ita ma jam’iyyar PDP ta ce ta isar da korafi ga rundunar ‘yan sanda, wadanda suka ce za su dauki matakin gaggauta ceto shi.

Idan ba a manta ba, watannin baya da suka wuce ma an sace shugaban jam’iyyar PDP dungurugum na jihar Ekiti, wanda tsohon Sanata ne.

Kafin a sako shi sai da aka biya makudan kudade.

Share.

game da Author