An maida Ali Janga ne a matsayin sa na Kwamishinan ’Yan sandan Kogi, kamar yadda kakakin rundunar ta jihar, William Aya ya tabbatar.
Aya ya battatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, cewa Janga ya koma aiki tun a ranar Talatar nan a bisa umarnin da Sufeto Janar Ibrahim Idris ya bayar.
Ya ce an maida kwamishinan ne bayan cikar wa’adin sati daya da aka ba shi na ya tabbatar da ya sake kamo wadanda suka tsere din nan daga hannun ‘yan sanda.
Sannan kuma Aya ya kara tabbatar da cewa mutanen shida da ake zargi da suka arce, tuni an samu nasarar sake kama su.
Ya kara yin bayanin cewa an kuma kama wasu mutane 13 a Lokoja, wadanda su ne suka taimaka musu har suka arce.
Ya ce wadanda aka kama din sun hada da direbobin Keke-NAPEP da suka dauke su, suka tsere da su, bayan sun arce, da kuma masu gidajen da suka boye su bayan da suka arce daga ofishin ‘yan sanda.
Discussion about this post