Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Rabiu Yusuf ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun kwatobindigogi da harsashen 60 daga hannun wadanda suka mallake su ba tare da lasisi ba
Ya fadi haka ne ranar Laraba da yake zantawa da menema labarai a garin Kano.
Mutane da kan su suka kawo mana makaman ganin wa’adin kwanakin da muka bada ayi haka ko mutum ya fuskanci hukunci ya cika.
Yusuf ya yi kira ga mutanen da basu dawo da makaman dake hannu su ba su hanzarta yin haka sannan duk wanda suka ga wani da bindiga ya gaggauta sanar wa ‘yan sanda.